Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Muslim Rights Concern (MURIC) - Ƙungiyar kare-Haƙƙin Musulmai
Muslim Students Society of Nigeria (MSSN) - Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai Ta Najeriya
Must - A turance tana nufin dole.
Misali; Dole ne dukkan musulmi ya yi sallah sau biyar a rana.
HAU; Dole (Tana nufin wajibi ko tilas)
Mutuntaka - Halaye da ɗabi'un kowane ɗan'adam, wadanda suke bambanta daga mutum zuwa mutum.
Mutuntakar Koyarwa - Ɓangare Ne Na Ilimin Koyarwa Da Ake Naƙaltar Mabambantan Ɗabi'u da Halayen Ɗalibai Ko Mutane.