Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Mix Something - A turance tana nufin kwaɓa. Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin. HAU; Kwaɓa (Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya)
Mix Thoroughly - A turance tana nufin cakuɗa. Misali; Amina tana cakuɗa kwaɗon zogale. HAU; Cakuɗa (Tana nufin a yi ta jujjuya abu)
Mix Together - A turance tana nufin gauraya. Misali; Ado ya gauraya garin dawar da rogo. HAU; Gauraya (Tana nufin cakuɗa abubuwa su zama ɗaya)
Mixture of flour and water - A turance tana nufin ƙullu. Misali: Mahaifiyata ta haɗa ƙullu za ta yi mana waina. HAU: Ƙullu (Tana nufin cakuɗa gari da ruwa da ake haɗawa domin yin wani abinci)
Mockery - A turance yana nufin ba'a. Misali; Lado ya yi wa Kande ba'a, ya ce mata mai ƙaton hanci. HAU; Ba'a (Tana nufin aibata mutum ko wata gaɓa ko wani sashe na halittarsa)
Modeling Agencies Association of Nigeria (MAAN) - Kadaurar Ƙungiyoyin Taurari Ta Najeriya
Modesty - A turance tana nufin kunya. Misali; Yarinyar tana da kunya da ɗa'a. HAU; Kunya (Tana nufin kawaici ko jin nauyin aikata lefi ko haɗa ido da mutane)    
Monday - Rana ce ta farko daga cikin ranakun mako.  Misali; Ranar Litinin zan fara zuwa makaranta. HAU: Litinin  
Money - A turance tana nufin kuɗi. Misali; Duk abin da za ka siya sai ka biya kuɗi tukunna. HAU; Kuɗi (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin cinikayya)
Monkey - A turance tana nufin biri. Misali; Da muka je gidan ajiye namun daji mun ga biri da kura. HAU; Biri (Tana nufin dabba mai yanayin siffar mutum)
1 4 5 6 7 8 9