Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Meat Fat - A turance tana nufin kakide.
Misali; Ina son babbar sallah ta zo don in samu kakide bayan an soya nama.
HAU; Kakide (Tana nufin kitsen da ake samu a jikin nama musamman bayan an soya)
Medical & Dentail Consultants Association of Nigeria (MDCAN) - Ƙungiyar Ƙwararrun Likitoci da Likitocin Hakori Ta Najeriya
Medical & Health Workers Union of Nigeria (MHWUN) - Ƙungiyar Likitoci da Malaman Lafiya Ta Najeriya
Meeting Suddenly - A turance tana nufin kaciɓis.
Misali; Mun yi kaciɓis da Gwaggo a kasuwa ɗazu.
HAU; Kaciɓis (Tana nufin haɗuwa ba zato ba tsammani)
Memorization - A turance tana nufin hadda.
Misali; Usman yana ajin hadda, za su sauke Ƙur'ani cikin shekara ɗaya.
HAU; Hadda (Tana nufin riƙe abu da ka)
Menstruation - A turance tana nufin haila.
Misali; Matan da ke haila ba sa shiga masallaci.
HAU; Haila (Tana nufin jinin da mata ke fitarwa a kowanne wata)
Mere - A turance tana nufin kacal.
Misali; Naira biyar kacal za ka biya ka ɗauki kayanka.
HAU; Kacal (Tana nufin kaɗai ko kaɗan)
Messy or disorderly - A turance tana nufin kaca-kaca.
Misali; Sun yi kaca-kaca da madara a ɗakin.
HAU; Kaca-kaca (Tana nufin a hargitse)
Metal Roof Drain - A turance tana nufin indararo.
Misali; Mun cika gidan nan da ruwan da muka tara a indararo.
HAU; Indararo (Tana nufin hanyar da ruwa yake zubowa ta saman rufin kwano)
Millet - A turance tana nufin gero.
Misali; Bana gero zalla ya shuka.
HAU; Gero (Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai wanda ake amfani da shi wajen yin fura da kunu da sauransu)