Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Mazayyana - Masu yin sana'ar zayyana
Maƙiyasta - Masu yin ƙiyasin ƙiɗiɗɗiga, kamar na adadin abubuwa da za a yi amfani da su tun daga farko farko har zuwa ƙarshen  aikin gini da makamantansu.
Measles - A turance tana nufin ƙyanda. Misali; Cutar baƙon dauro ta yi sanadiyyar mutuwar yara da yawa a karkararmu. HAU; Ƙyanda (Tana nufin cutar ƙyanda, wadda ƙananan ƙuraje ke fitowa a jiki gaba ɗaya. Idan ta yi tsamari tana haddasa kurumta, makanta da sauransu)
Medical & Dentail Consultants Association of Nigeria (MDCAN) - Ƙungiyar Ƙwararrun Likitoci da Likitocin Hakori Ta Najeriya
Medical & Health Workers Union of Nigeria (MHWUN) - Ƙungiyar Likitoci da Malaman Lafiya Ta Najeriya
Ministry - Ma'aikata
Ministry of Police Affairs - Ma'aikatar Harkokin 'Ƴansanda
Mockery - A turance yana nufin ba'a. Misali; Lado ya yi wa Kande ba'a, ya ce mata mai ƙaton hanci. HAU; Ba'a (Tana nufin aibata mutum ko wata gaɓa ko wani sashe na halittarsa)
Modeling Agencies Association of Nigeria (MAAN) - Kadaurar Ƙungiyoyin Taurari Ta Najeriya
Monday - Rana ce ta farko daga cikin ranakun mako.  Misali; Ranar Litinin zan fara zuwa makaranta. HAU: Litinin  
1 2 3 4 5