Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Make Slushy - A turance tana nufin caɓa.
Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai.
HAU; Caɓa (Tana nufin yin ado da yawa)
Makimanta - Masu kimanta darajar ƙasa ko gida, musamman wajen kimanta darajar muhalli.
Male Hyena - A turance tana nufin kure.
Misali; Auwalu ya kamo kure, da shi yake wasa ranar kasuwa.
HAU; Kure (Tana nufin namijin kura)
Man’s charm worn around the arm - A turance tana nufin kambu.
Misali; Gaba ɗaya mafarautan suna ɗauke da kambu a hannunsu.
HAU; Kambu (Tana nufin wani nau'in surkulle da maza ke ɗaurawa a hannu musamman mafarauta da 'yan dambe)
manufacturers Association of Nigeria (MAN) - Ƙungiyar Kamfanonin Ƙere-Ƙere-Ta Najeriya
Marawaita - 'Yan rahoto, masu hadawa da kawo rahoto game da wani abu ko wata ma'aikata.
March - A turance yana nufin wata na uku a shekara
Misali;Adamu zai koma sabon gidansa a watan Maris.
HAU; Maris (Wata ne na uku a shekara)
Maris - Wata ne na uku a shekara.
Misali;Adamu zai koma sabon gidansa a watan Maris.
ENG; March (A turance yana nufin wata na uku a shekara)
Maritime Workers Union of Nigeria (MWUN) - Ƙungiyar Ma'aikatan Gaɓar Tekun Najeriya
Masarrafa - Masu sarrafawa ko hada wani abu kamar abin ci ko magani domin amfanin jama'a.