Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kurum - Tana nufin kawai.
Misali; Kwano ɗaya kurum ta isa kowa ya ƙoshi.
ENG; Only (A turance tana nufin kurum)
Kururuwa - Tana nufin ihu da ƙarfi.
Misali; Sadiƙ yana da rowa idan aka ɗauki abinsa kururuwa yake.
ENG; Shouting (A turance tana nufin kururuwa)
Kusa - Tana nufin dab da.
Misali; Ana siyar da wainar gero a kusa da gidanmu.
ENG; Near (A turance tana nufin kusa)
Kushe - Tana nufin faɗar aibu ko ƙaƙalo laifin abu.
Misali; Duk yanda abu ya kai da kyau mahassada sai sun kushe shi.
ENG; Find Fault (A turance tana nufin kushe)
Kushewa - Tana nufin kabari.
Misali; An kai ta kushewa tun safe da aka yi jana'izarta.
ENG; Grave (A turance tana nufin kushewa)
Kushin - Tana nufin kujerar bature.
Misali; Hedimasta yana zaune a kan kushin ɗin ofishinsa a lokacin da muka kai masa ziyara.
ENG; Cushion (A turance tana nufin kushin)
Kuskure - Tana nufin yin abu ba daidai ba.
Misali; Idan mutum ya yi kuskure ya kamata a yi masa afuwa.
ENG; Failure (A turance tana nufin kuskure)
Kusu - Tana nufin ɓera.
Misali; Na ga kusu a cikin ɗakin ajiya, dole sai mun sa magani.
ENG; Rat/Mouse (A turance tana nufin kusu)
Kusurwa - Tana nufin kwana.
Misali; Na ajiye adakar a kusurwar ɗakin da muke kwana.
ENG; Corner (A turance tana nufin kusurwa)
Kutsa - Tana nufin shiga da ƙyar.
Misali; Ya kutsa cikin taron don ya ga gwamnan garinsu.
ENG; Squeeze Through (A turance tana nufin kutsa)