Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kurga - Tana nufin koren kashi mai kumfa wanda yaran da ake shayarwa ke yi.
Misali; Tana shirin yaye ɗanta ya fara kurga.
ENG; Diarrhoe In Children (A turance tana nufin kurga)
Kuri - Tana nufin cika baki ko kambama kai.
Misali; Safiyanu ya cika kuri, amma ana taɓa shi zai fara kuka.
ENG; Boasting (A turance tana nufin kuri)
Kurkudu - Tana nufin wani ƙwaro da yake fitowa a cikin rairayi.
Misali; Yaran sun kamo kurkudu a lokacin da suke wasa.
ENG; Sand Lice (A turance tana nufin kurkudu)
Kurkuku - Tana nufin inda ake ajiye masu laifi, waɗanda aka yankewa hukunci da masu jiran hukunci.
Misali; Jami'an sun tafi da masu laifin kurkuku.
ENG; Prison (A turance tana nufin kurkuku)
Kurkunu - Tana nufin cutar fata mai sanya ƙuraje.
Misali; An yi nasarar kawar da cutar kurkunu a Najeriya.
ENG; Guinea-worm (A turance tana nufin kurkunu)
Kurkure - Tana nufin zuba ruwa a jujjuya shi a cikin baki da zimmar ɗurayewa.
Misali; Idan za a yi alwala ana kurkure baki sau uku ne.
ENG; Rinse (Mouth) (A turance tana nufin kurkure)
Kurma - Tana nufin mai ɗauke da lalurar rashin ji.
Misali; Tun yana yaro ya zama kurma sakamakon ciwon baƙon dauro da ya yi.
ENG: Deaf person (A turance tana nufin kurma)
Kurmi - Tana nufin ƙungurmin daji.
Misali; Jami'an tsaro sun kame ɓarayin da ke kurmi gaba ɗaya.
ENG; Thick Forest (A turance tana nufin kurmi)
Kurna - Tana nufin bishiya mai ƙaya mau ɗauke da ƙananan 'ya'ya masu zaƙi waɗanda ake sha.
Misali; 'Ya'yan kurna suke sha kullum idan sun je makaranta.
ENG; A thorny tree with edible berries (A turance tana nufin kurna)
Kurtu - Tana nufin ƙaramin mazubi na duma.
Misali; Maharazu ya zuba tawada a cikin kurtu.
ENG; Small Round Gourd (A turance tana nufin kurtu)