Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kuntu - Tana nufin bargo launin ruwan ƙasa wanda sojoji suke amfani da shi.
Misali; An raba musu kuntu a ranar da suka shiga daji don yaƙi da 'yan ta'adda.
ENG; Brown blanket used by army personnel (A turance tana nufin kuntu)
Kuntukuru - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa.
Misali; Na jiyo sautin kuntukuru, da alama an fara wasan.
ENG; Small bowl-shaped drum which is hung from the neck and beaten with small flexible sticks (A turance tana nufin kuntukuru)
Kunu - Tana nufin abin sha wanda ake yi da gari ko markaɗaɗɗen gero mai ƙunshe da kayan ƙamshi da tsamiya ko kanwa.
Misali; An dama wa mai jego kunu.
ENG; Gruel made of guinea-corn or millet flour (A turance tana nufin kunu)
Kunya - Tana nufin kawaici ko jin nauyin aikata lefi ko haɗa ido da mutane.
Misali; Yarinyar tana da kunya da ɗa'a.
ENG; Modesty (A turance tana nufin kunya)
Kunya - Tana nufin dogwayen tudu-tudun da ke gona.
Misali; Iro ya noma kunya bakwai yau a gona.
ENG; Ridge-row on farm (A turance tana nufin kunya)
Kura - Tana nufin wata dabbar daji mai cin ɗanyen nama.
Misali; Mafarautan sun kamo kura.
ENG; Hyena (A turance tana nufin kura)
Kuratandu - Tana nufin mazubin kwalli wato mazubin da ake adana kwalli a ciki.
Misali; Inna Hajjo ta kawo wa mai jego kyautar kurantandu cike da farin kwalli.
ENG: Small hide container (A turance tana nufin kuratandu)
Kurciya - Tana nufin ƙaramar tsuntsuwa.
Misali; Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali ke ganewa.
ENG; Small Dove (A turance tana nufin kurciya)
Kure - Tana nufin namijin kura.
Misali; Auwalu ya kamo kure, da shi yake wasa ranar kasuwa.
ENG; Male Hyena (A turance tana nufin kure)
Kurege - Tana nufin wata dabba mai kama da zomo.
Misali; Ado ya bi kurege har cikin raminsa ya kamo shi.
ENG; Ground Squirrel (A turance tana nufin kurege)