Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kumatu - Tana nufin jam'in kunci wato gefen fuska na hagu ko na dama.
Misali; Fauziya ta shafa hoda a kumatu.
ENG; Cheeks (A turance tana nufin kumatu)
Kumbon Sadarwa - Tauraron dan'adam, wato kumbon da ake harbawa zuwa sararin sama ko wata duniyar domin sadarwa, musamman ta radiyo da waya da tattaro bayanai.
Kumbura - Tana nufin ƙara girma ko tashi sakamakon bigewa ko jin ciwo.
Misali; Ƙafarsa ta kumbura lokacin da ya ji ciwo a filin ƙwallo.
ENG; Swell (A turance tana nufin kumbura)
Kumfa - Tana nufin wani farin abu mara nauyi da yake tasowa idan an kaɗa sabulu a ruwa ko kuma idan an juye lemo mai gas ko a kogi idan ruwa ya hautsine.
Misali; Ai dole wankin nan ya fita don sabulun yana da kumfa sosai.
ENG; Foam/Froth (A turance tana nufin kumfa)
Kumurci - Tana nufin baƙin maciji mai dafi.
Misali; Kumurci ya sari kaka a gona.
ENG; Black-hooded Cobra (A trurance tana nufin kumurci)
Kunama - Tana nufin ƙwaro mai cizo kuma mai dafi.
Misali; Kunama ce ta harbi Lado a ƙafa.
ENG; Scorpion (A turance tana nufin kunama)
Kunci - Tana nufin gefen fuska na hagu ko na dama.
Misali; Ya sha mari a gefen kuncinsa na hagu.
ENG; Cheek (A turance tana nufin kunci)
Kunkuru - Tana nufin wata dabba mai rayuwa a ruwa ko a doron ƙasa ko kuma guri mai danshi, tana tafiya a hankali kuma yana rayuwa mai tsayi.
Misali; Kunkuru yana iya rayuwa sama da shekaru tamanin ba doron ƙasa.
ENG; Tortoise (A turance tana nufin kunkuru)
Kunne - Tana nufin gaɓar da ake ji da ita.
Misali; Yara na yawan yin ciwon kunne musamman lokacin sanyi.
ENG; Ear (A turance tana nufin kunne)
Kuntigi - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa.
Misali; Na jiyo kiɗan kuntigi a ƙofar gidan maigari.
ENG; Small one-stringed plucked musical instrument (A turance tana nufin kuntigi)