Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kukuma - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya. Misali; Makaɗan kukuma suna da baiwa ta musamman. ENG; Small one stringed bowed musical instrument (A turance tana nufin kukuma)
Kula - Tana nufin mayar da hankali a kan abu. Misali; Idan za ki tsallaka titi ki kula saboda motoci na wucewa da gudu. ENG; Pay Attention (A turance tana nufin kula)
Kule - Tana nufin mage. Misali; Gidansu Hanan suna da ƙaton kule. ENG; Cat (A turance tana nufin mage)
Kulki - Tana nufin gajeren sanda mai kauri wanda 'yan doka suke riƙewa. Misali; Ɗan dokar na riƙe da kulki lokacin da suka je kama ɓarayin. ENG; Cudgel (A turance tana nufin kulki)
Kulle - Tana nufin rufewa. Misali; Lokacin da muka je an kulle ƙofar saboda mun makara. ENG; Lock (A turance tana nufin kulle)
Kullum - Tana nufin kowacce rana. Misali; Mukan yi salla sau biyar a kullum. ENG; Every Day (A turance tana nufin kullum)
Kulob - Tana nufin ƙungiya. Misali; Jibrin ɗan ƙungiyar Hausa ne a makaranta. ENG; Club (A turance tana nufin kulob)
Kulɓa - Tana nufin dabba mai kama da ƙadangare amma jikinta yana da santsi kuma tana da launuka daban-daban, tana rayuwa a cikin ciyayi. Misali; Na ga kulɓa a filin da muke wasa a makaranta. ENG; Skink Lizard (A turance tana nufin kulɓa)
Kuma - Tana nufin sake yi ko maimaitawa. Misali; Yanzu zazzaɓi ba ya jin magani ko kin sha sai kin kuma sha. ENG; Repeat (A turance tana nufin kuma)
Kumama - Tana nufin mutum mai saurin jin sanyi. Misali; Sadiq kumama ne, ko yaya aka yi ruwa sai ya sa rigar sanyi. ENG; Person of weak physical constitution (A turance tana nufin kumama)
1 18 19 20 21 22 26