Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kada - Tana nufin wata dabbamai kaushin baya kuma mai siffar ƙadangare da ke rayuwa a ruwa, amma tana da girma ainun.
Misali; Ruwan sama mai yawa ya sa kada ta fito daga gidan ajiyar namun daji.
ENG; Crocodile (A turance tana nufin kada)
Kadara - Tana nufin kaya masu daraja ko kayan kuɗi.
Misali; Sun buƙaci ya kawo takardun wata kadara kafin su ba shi rancen kuɗi.
ENG; Property (A turance tana nufin kadara)
Kadarko - Tana nufin ƙaramar gada da ake yi da katako musamman don kwararar ruwa.
Misali; A hanyar gidan maigari akwai kadarko.
ENG; Small Bridge (A turance tana nufin kadarko)
Kadaura - Babbar kungiya ko cibiya wadda ta hado mahimman bangarori masu zaman kansu ko kwararrun ma'aikata ko mutane.
Kaf - Tana nufi duka ko gaba ɗaya.
Misali; Ta kwashe kayanta kaf daga gidan, kun ga kenan ba ta niyyar dawowa.
ENG; Completely (A turance tana nufin kaf)
Kafa - Tana nufin ƙaramar hanya.
Misali; Ko yaya ɓeran ya samu kafa guduwa zai yi.
ENG; Small Hole (A turance tana nufin kafa)
Kafafen Intanet - Matattara ko inda ake samun bayanan da aka nema daga rumbon sadarwa.
Kafaɗa - Tana nufin sashen jiki da ke saman hannu.
Misali; 'Yan mata na rawar girgiza kafaɗa a dandali.
ENG; Shoulder (A turance tana nufin kafaɗa)
Kaffara - Tana nufin abin da mutum zai yi don karya rantsuwa ko sakamakon kisa da sauransu. Akan yi kaffara da azumi ko ciyarwa da sauransu.
Misali; Azumi uku ake yi a kaffarar rantsuwa.
ENG; Penalty to atone for breaking certain islamic law (A turance tana nufin kaffara)
Kafi - Tana nufin surkulle ko abin da ake sa wa a gida domin kariya daga ɓarayi ko rashin sa'a.
Misali; Akwai kafi a saman soron gidan.
ENG; Charm buried in front of door way or inside house for protection against misfortune (A turance tana nufin kafi)