Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kucaki - Tana nufin mutum mara tsafta.
Misali; Wani kucaki ne a bakin kasuwa yake siyar da gwangwanaye.
ENG; Slovenly Person (A turance tana nufin kucaki)
Kudu - Tana nufin wani ɓangare daga cikin ɓangarori.
Misali; Gabas ake kallo idan za a yi salla ba kudu ba.
ENG; South (A turance tana nufin kudu)
Kududdufi - Tana nufin ƙaton rami da ake samu a ƙauyuka da bayan gari, idan damina ta zo yakan cika da ruwa. Bayan damina kuma akan ɗibi yashi ko ƙasar gurin a yi amfani da ita.
Misali; Kafin mutane su yi gine-gine ƙaton kududdufi ne a gurin.
ENG; Burrow-Pit (A turance tana nufin kududdufi)
Kufai - Gurbi na ramuka ko koguna ko gine-ginen da suke nuna cewar mutane sun taba wanzuwa/zama a wurin a zamunnan baya.
Kufta - Tana nufin taguwa mai tsayin da ya haura gwuiwa, tana da aiki a wuyan da bakin aljihu da kuma hannun rigar.
Misali; Ɗinkin kufta ya yi tsada ba kowa ne yake iya yi ba.
ENG; A three-quarter length taguwa with embroidery around the neck and sleeves (A turance tana nufin kufta)
Kuje - Tana nufin jin ciwo a saman fata.
Misali; Amir ya faɗi ya kuje a gwuiwa.
ENG; Scratch (A turance tana nufin kuje)
Kujera - Tana nufin abin da ake zama a kai.
Misali; Inna ta siyo sabuwar kujera.
ENG; Chair (A turance tana nufin kujera)
Kuka - Tana nufin koren ganyen bishiyar da ake amfani da shi don yin miya, yana da sinadarai masu matuƙar amfani a jiki.
Misali; Miyar kuka na ɗaya daga cikin miyoyin Hausawa na gargajiya.
ENG; Baobab Tree (A turance tana nufin kuka)
Kuka - Tana nufin zubar hawaye daga idanu sakamakon murna ko ɓacin rai.
Misali; Safiya ta sha kuka lokacin da mahaifinta ya rasu.
ENG; Crying (A turance tana nufin kuka)
Kuku - Tana nufin wanda yake aikin dafa abinci.
Misali; Gidan attajirai ne ake ajiye kuku.
ENG; Cook (A turance tana nufin kuku)