Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kora - Tana nufin nau'in cutar fata da yake fitowa a kai. Misali; Yana da kora, idan ka sa hularsa za ka iya ɗauka kuma lalura ce mai wuyar sha'ani. ENG; Scalp Disease (A turance tana nufin kora)
Kore - Tana nufin launi. Misali; Kayan makarantarsu kore ne. ENG; Green (A turance tana nufin kore)
Kotso - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa. Misali; Ya daɗe yana kaɗa kotso a ƙauyensu. ENG; Open-ended variable tone drum which is beaten with fingers (A turance tana nufin kotso)
Kotu - Tana nufin gurin da ake gudanar da shari'a. Misali; Lauyoyin sun fito harabar kotu domin su huta kafin shiga shari'a ta gaba. ENG; Court (A turance tana nufin kotu)
Kowa - Tana nufin mutane baki ɗaya. Misali; Kowa zai iya neman tallafin da gwamnati take bayarwa. ENG; Everyone (A turance tana nufin kowa)
Koyar - Tana nufin sanar da mutum ilimi. Misali; Malam Musa Ya koyar da mu darasin lissafi. ENG; Teach (A turance tana nufin koyar)
Koyaushe - Tana nufin kowane lokaci. Misali; Kakarmu tana ibada a koyaushe. ENG; Always (A turance tana nufin koyaushe)
Koyaya - Tana nufin duk ƙaranci. Misali; Koyaya mutum ya samu ilimi zai masa amfani. ENG; No Matter How (A turance tana nufin koyaya)
Koyi - Tana nufin kwaikwaya ko yin abinda wani ya yi. Misali; Koyi da annabawa kyakkyawar ɗabi'a ce. ENG; Imitate (A turance tana nufin koyi)
Koɗe - Tana nufin canja yanayi ko launi musamman sakamakon jin jiki.  Misali; Atamfar ta koɗe saboda ta sha wanki a kai a kai. ENG; Fade (A turance tana nufin koɗe)
1 16 17 18 19 20 26