Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kofato - Tana nufin ƙafar dabba kamar saniya ko akuya ko doki. Misali; Na ga shatin kofato da alama doki ya bi ta nan gurin. ENG; Hoof (A turance tana nufin kofato)
Kogi - Tana nufin ruwa mai gudana. Misali; An tsinci jariri a bakin kogi ranar Asabar. ENG; River (A turance tana nufin kogi)
Kogo - Tana nufin wani wawakeken rami da ke jikin bishiya kamar ta kuka, tsamiya da sauransu. Misali; Karnukan sun shige cikin kogon bishiya a gonar da ke bayan gari. ENG; Hollow of tree (A turance tana nufin kogo)
Kokawa - Tana nufin ɗaya daga cikin wasannin gargajiya, inda maza biyu ke doke-doke a tsakaninsu har a kayar da ɗaya. Misali; Su Lado sun tafi kallon kokawa a dandali. ENG; Wrestling (A turance tana nufin kokawa)
Koko - Tana nufin abin sha da ake yi da gero, ana dama shi da tafasasshen ruwa kamar kunu. Misali; Koko da ƙosai ɗaya ne daga cikin abincin karin kumallon Hausawa. ENG; Millet Porridge (A turance tana nufin koko)
Koko-koke - Tana nufin jam'in kuka. Misali; Na jiyo ana ta koke-koke a gidan mutuwar, Allah ya gafarta masa da rahama. ENG; Cries (A turance tana nufin koke-koke)
Kokwanto - Tana nufin yin wasi-wasi ko tunanin abu daidai ne ko ba daidai ba, zai yiwu ko ba zai yiwu ba. Misali; Tun safe nake kokwanton fita, kar in fita ruwa ya sakko don akwai gagarimin hadari. ENG; Doubt (A turance tana nufin kokwanto)
Kolanut - A turance tana nufin goro. Misali; An raba goro a gurin ɗaurin auren. HAU; Goro (Tana nufin ɗan itaciya da ake ci mai ƙunshe da muhimman abubuwa masu inganci)
Kolo - Tana nufin nau'in abin kiɗa mai kama da jauje. Misali; Malam Habu makaɗin kolo ne sama da shekaru ashirin da suka wuce. ENG; Drum similar to jauje (A turance tana nufin kolo)
Koma - Tana nufin abin da masunta suke amfani da shi wajen kama kifi. Misali; Akwai koma a cikin jakar da yake tafiya SU da ita. ENG; Fishing Net (A turance tana nufin koma)
1 15 16 17 18 19 26