Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kitso - Tana nufin salon tufke gashi don ado da kwalliya.
Misali; Mata su ne ke yin ado da kitso da ƙunshi.
ENG; Plaiting Of Hair (A turance tana nufin kitso)
Kiwata - Tana nufin ciyarwa ta tsahon lokaci.
Misali; Zan kiwata Saniyar da aka ba ni har ta hayayyafa.
ENG; Feed Animal (A turance tana nufin kiwata)
Kiwo - Tana nufin ciyar da dabbobi kamar awaki da shanu da kaji da sauransu.
Misali; Sana'ar kiwo ta karɓi Malam Iro, garkensa sai haɓaka yake kullum.
ENG; Tending animal at pasture (A turance tana nufin kiwo)
Kiyama - Tana nufin ranar tsayuwa, wato ranar da za a tashi ababen halitta a yi musu hisabi.
Misali; Allah SWT shi ya san ranar da kiyama za ta tashi.
ENG; Day Of Resurrection (A turance tana nufin kiyama)
Kiyashi - Tana nufin ɗan ƙaramin ƙwaro mara cizo.
Misali; Kiyashi ya lulluɓe naman da na ɓoye a cikin ƙwarya.
ENG; Small Ant (A turance tana nufin kiyashi)
Kiɗa - Tana nufin rauji ko sauti mai daɗi.
Misali; Matasan sun kunna kiɗa suna cashewa don murnar bikin abokinsu.
ENG; Music (A turance tana nufin kiɗa)
Kiɗime - Tana nufin gigicewa ko shiga wani hali.
Misali; Duk sun kiɗime saboda tashin hankali.
ENG; Confused/Flustered (A turance tana nufin kiɗime)
Knee - A turance tana nufin gwiwa.
Misali; Ciwon gwiwa yake yi tunda shekarunsa suka ja.
HAU; Gwiwa (Tana nufin sashen jiki da ke tsakanin ƙafa da cinya)
Kneel with front elbows on ground - A turance tana nufin gurfana.
Misali; Masu laifin sun gurfana a gaban alƙali.
HAU; Gurfana (Tana nufin durƙusawa a kan gwuiwa biyu)
Knowledge - A turance tana nufin ilimi.
Misali; Allah ya yi masa baiwar ilimi ƙwarai da gaske.
HAU; Ilimi (Tana nufin sani)