Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kirista - Tana nufin mabiya addinin kiristanci wato ahalil kitabi. Misali; Makociyata kirista ce, kuma muna zaman lafiya sosai. ENG; Christian (A turance tana nufin kirista)
Kirki - Tana nufin kyautatawa ko hali mai kyau. Misali; Yin tarayya da mutanen kirki na sa mutum ya zama mai nagarta. ENG; Kindness (A turance tana nufin kirki)
Kirsimeti - Tana nufin bikin zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu. Misali; Kiristoci na bikin kirsimeti a duk ranar 25 ga watan Disamba. ENG; Christmas (A turance tana nufin kirsimeti)  
Kirɓa - Tana nufin daka abu sosai a cikin turmi. Misali; Za mu kirɓa sakwara a ranar bikin da yardar Allah. ENG; Pound (A turance tana nufin kirɓa)
Kisa - Tana nufin ɗaukar rai. Misali; 'Yan ta'adda sun mayar da kisa ba komai ba a Najeriya. ENG; Killing (A turance tana nufin kisa)
Kishi - Tana nufin sosuwar zuciya da ɓacin ran da suke jawo fushi, a dalilin tarayyar da wani ya yi da wani, a kan abin da wanin ya keɓanta da son sa koma mallakarsa. Misali; Matan wannan zamani na da matuƙar kishi wanda ya saɓawa shari'a. ENG; Jealousy (A turance tana nufin kishi)
Kishiya - Tana nufin abokiyar zama wadda aure ya haɗa, ma'ana idan mutum yana da mata biyu, ɗaya kishiyar ɗaya ce. Misali; An yi wa Lantana kishiya satin da ya wuce. ENG; Co-wife (A turance tana nufin kishiya)
Kissa - Tana nufin yin amafani da wayo da dabara da hilata don cimma manufa. Misali; Ba asiri ta yi wajen fitar da abokiyar zamanta ba, kissa ce da kisisina. ENG; Using clever or deceitful means for some purpose (A turance tana nufin kissa)
Kitchen - A turance tana nufin kicin. Misali; Hamida tana taya Umma girki a kicin. HAU; Kicin (Tana nufin ɗakin girki)
Kitse - Tana nufin maiƙon da ke jikin nama. Misali; Ragon yana da kitse ainun, maiƙon jikinsa ya isa a soya shi. ENG; Fat On Meat (A turance tana nufin kitse)
1 13 14 15 16 17 26