Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kilogiram - Tana nufin ma'aunin nauyi.
Misali; Nauyin buhun shinkafa kilogiram hamsin ne.
ENG; Kilogram (A turance tana nufin kilogiram)
Kilogram - A turance tana nufin kilogiram.
Misali; Nauyin buhun shinkafa kilogiram hamsin ne.
HAU; Kilogiram (Tana nufin ma'aunin nauyi)
Kilometer - A turance tana nufin kilomita.
Misali; Nisan Jihar Kano zuwa jihar Legas ya kai kusan kilomita dubu.
HAU; Kilomita (Tana nufin ma'aunin nisan tafiya)
Kilomita - Tana nufin ma'aunin nisan tafiya.
Misali; Nisan Jihar Kano zuwa jihar Legas ya kai kusan kilomita dubu.
ENG; Kilometer (A turance tana nufin kilomita)
Kindirmo - Tana nufin Nonon da ya kwana ya yi kauri.
Misali; Ina son shan kindirmo da safe.
ENG; Youghurt (A turance tana nufin kindirmo)
Kindness - A turance tana nufin kirki.
Misali; Yin tarayya da mutanen kirki na sa mutum ya zama mai nagarta.
HAU; Kirki (Tana nufin kyautatawa ko hali mai kyau)
Kintsa - Tana nufin tattara kaya guri ɗaya.
Misali; Kar ki fita sai kin kintsa ɗakin tunda kin bari yara sun hargitsa shi.
ENG; Tidy Up (A turance tana nufin kintsa)
Kintsattse - Tana nufin mutum mai kamala da nutsuwa.
Misali; Ai da ganinsa an ga kintsattse, don kamanninsa sun nuna haka.
ENG; Polite (A turance tana nufin kintsattse)
Kirari - Tana nufin maganganun da ake yi wa mutum ko mutane don kwarzantawa ko kambamawa.
Misali; A kodayaushe akan yi wa mafarauta kirari kafin su tafi farauta.
ENG; Praise (A turance tana nufin kirari)
Kirci - Tana nufin wasu ƙuraje masu matuƙar ƙaiƙayi da ke fitowa a fata sakamakon rashin tsabta.
Misali; Abin da yasa almajirai ke yin kirci shi ne rashin wanka.
ENG; Eczema (A turance tana nufin kirci)