Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kewa - Tana nufin son gani ko kasancewa da wanda ba ya kusa ko ya rasu. Misali; Idan mutum ya rasu akan kasance cikin kewarsa a kodayaushe. ENG; Missing Someone (A turance tana nufin kewa)
Keɓe - Tana nufin warewa gefe. Misali; Sun keɓe suna tattaunawa saboda batun yana da muhimmanci. ENG; Set Aside (A turance tana nufin keɓe)
Khaki Cloth - A turance tana nufin kaki. Misali; Dole ne ka ji tsoron mai kaki don ka san soja ba abin wasa ba ne. HAU; Kaki (Tana nufin kayan sojoji)
Kibiya - Tana nufin abin da ake ƙerawa, ana mafani da ita don yin harbi. Misali; Jarumin ya harba kibiya a ƙirjin dokin. ENG; Arrow (A turance tana nufin kibiya)
Kicin - Tana nufin ɗakin girki. Misali; Hamida tana taya Umma girki a kicin. ENG; Kitchen (A turance tana nufin kicin)
Kifi - Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin ruwa. Misali; San'ar kifi sana'a ce mai albarka. ENG; Fish (A turance tana nufin kifi)
Kilaki - Tana nufin (karuwa) mace mai zaman kanta. Misali; Kowa ya san tsohuwar kilaki ce, sai dai mu ce Allah ya shirye mu duka. ENG; Harlot (A turance tana nufin karuwa)
Kilisa - Tana nufin hawa dokuna don nishaɗi. Misali; An shirya kilisa a bikin angwancin Abdullahi. ENG; Horse-riding for pleasure (A turance tana nufin kilisa)
Kilishi - Tana nufin nama wanda aka sarrafa shi da kayan ƙamshi kuma aka busar da shi a rana. Misali; A Unguwar Agadasawa ana siyar da kilishi da dambun nama. ENG; Meat coated with spices and dried in the sun (A turance tana nufin kilishi)
Killing - A turance tana nufin kisa. Misali; 'Yan ta'adda sun mayar da kisa ba komai ba a Najeriya. HAU; Kisa (Tana nufin ɗaukar rai)
1 11 12 13 14 15 26