Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kaɗai - Tana nufin kawai.
Misali; Ita kaɗai ce take zuwa da wuri kullum.
ENG; Only (A turance tana nufin kaɗai)
Kaɗaita - Tana nufin ɗayantawa ba tare da abokin tarayya ba musamman ga Allah SWT.
Misali; Wajibi ne a kaɗaita Allah a wajen bauta.
ENG; Oneness (A turance tana nufin kaɗaita)
Kaɗan - Tana nufin babu yawa.
Misali; Sun yi aiki mai yawa amma ya ba su kuɗi kaɗan.
ENG; Few (A trurance tana nufin kaɗan)`
Kishiyarta; Da yawa
Kaɗanya - Tana nufin 'ya'yan bishiyar kaɗe.
Misali; Man kaɗanya na gyara fata musamman a lokacin sanyi.
ENG; Shea Tree (A turance tana nufin kaɗanya)
Kaɗi - Tana nufin sana'ar sarrafa auduga.
Misali; Na taso na ga kakata tana sana'ar kaɗi, amma yanzu sana'ar ta zama ta zamani.
ENG; Spinning (A turance tana nufin kaɗi)
Kaɗo - Tana nufin wanda ba bafulatani ba.
Misali; Fulani ba sa son 'ya'yansu su auri kaɗo.
ENG; A person who has no Fulani ancestry (A turance tana nufin kaɗo)
Keji - Tana nufin (akurki) wani abu da ake haɗa shi da rodi ko wayoyi, ana amfani da shi wajen killace dabbobi.
Misali; An zuba kajin a keji za a ba su abinci.
ENG; Cage (A turance tana nufin keji)
Kerosene - A turance tana nufin kananzir.
Misali; Zamani ya sa an dena amfani da kananzir sosai.
HAU; Kananzir (Tana nufin makamashin da ake amfani da shi wajen girki da kunna fitila)
Keso - Tana nufin tsohuwar tabarmar kaba.
Misali; An ɗora buhun geron a kan keso.
ENG; Worn-out palm-leaf mat (A turance tana nufin keso)
Kettle - A turance tana nufin buta.
Misali; Na siyo sabuwar buta a kasuwar da na je.
HAU; Buta (Tana nufin mazubin ruwa musamman don yin alwala)