Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gida - Tana nufin mazauni ko gini da ake yi don ba wa kai kariya daga abin cutarwa. Misali; Ya gina ƙaton gida a sabuwar unguwa. ENG: House (A turance tana nufin gida)
Gidan Rediyon Caina/Sin - China Radio International (CRI)
Gidan Rediyon Faransa - Radio France International (RFI)
Gidauniyar Cinikayya Ta Najeriya da Amurka - Nigerian American Chamber of Commerce (NACC)
Gidauniyar Haɗin Guiwar Bunƙasa Sabuwar Afirka - New Partnership for Africa's Development (NEPAD)
Gidauniyar Kyautata Tattalin Arziki da Zumunta - Socio-Economic Rights & Accountability Project (SERAP)
Gift from God - A turance tana nufin baiwa. Misali; Yaran aji ɗaya suna da baiwa ta musamman, don suna saurin gane karatu. HAU; Baiwa (Tana nufin wani abu na musamman da Allah yake ba wa bayinsa wanda ya bambanta su da sauran mutane)
Gifta - Tana nufin wucewa ta gaban abu. Misali; Na ga Iliya ya gifta ɗazu. ENG: Cross In Front (A turance tana nufin gifta)
Giginya - Tana nufin ɗaya daga cikin 'ya'yan itaciya masu amfani ga ɗan Adam, kama daga ƙwallonta da ganyenta da ma ita kanta. Misali; Gingiya tana da zaƙi da kuma maganin basir. ENG; Deleb Palm (A turance tana nufin giginya)
Ginger - A turance tana nufin citta. Misali; An zuba wadatacciyar citta a yajin. HAU; Citta (Tana nufin ɗaya daga cikin sinadaran abinci mai inganci ga lafiya, tana da yaji, kuma akwai ɗanya akwai busasshiya)
1 7 8 9 10 11 19