Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gemu - Tana nufin gashin da yake fitowa a haɓar maza.
Misali; Ya aske gemunsa ranar Lahadi.
ENG; Beard (A turance tana nufin gemu)
General - A turance tana nufin janar.
Misali; Ya kai matakin Janar a aikin soja yanzu.
HAU; Janar (Tana nufin babban muƙamin soja)
Generator - A turance tana nufin janareto.
Misali; Rashin wuta ya sa janareto ya yi tsada matuƙa.
HAU; Janareto (Tana nufin injin da ke bayar da wutar lantarki idan an sa masa fetur)
Generous - A turance tana nufin karimi.
Misali; Masha Allah ai Alhaji karimi ne ƙwarai da gaske.
HAU; Karimi (Tana nufin mutum mai girma da darajta mutane tare da kyautata musu)
Gentle person - A turance tana nufin kamili.
Misali; Malam Musa kamili ne.
HAU; Kamili (Tana nufin nagartaccen mutum mai kyawawan halaye)
Gero - Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai wanda ake amfani da shi wajen yin fura da kunu da sauransu.
Misali; Bana gero zalla ya shuka.
ENG; Millet (A turance tana nufin gero)
Gewaye - Tana nufi yi wa abu ƙawanya.
Misali; Ya gewaye gonarsa da kara saboda gudun dabbobi.
ENG; Surround (A turance tana nufin gewaye)
Ghost - A turance tana nufin fatalwa.
Misali; An ce fatalwar Idi tana fitowa da daddare.
HAU; Fatalwa (Tana nufin wanda ya mutu ya dinga gizo)
Giant Male Rat - A turance tana nufin burgu.
Misali; Da zan je makaranta na ga wani burgu ya shige rami da gudu.
HAU; Burgu (Tana nufin jibgegen namijin ɓera)
Giant Rat - A turance tana nufin gafiya.
Misali; Ramin gafiya ne a gurin.
HAU; Gafiya (Tana nufin ƙaton ɓera)