Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gaya - Tana nufin tsura ko tsirara.
Misali; Ta dama min fura gaya, ba nono bare suga.
ENG; Naked State (A turance tana nufin gaya)
Gayauna - Tana nufin wani sashi na gona da ake ba wa matasa don su noma.
Misali; An ba wa Ɗahiru gayauna saboda ya samu kuɗin hidimar bikin kalankuwa.
ENG; Small patch or plot of land given to a young boy to farm on (A turance tana nufin gayauna)
Gaye - Tana nufin matashi wanda yake shiga irin ta turawa.
Misali; Ai yanzu ya zama gaye, kullum za ka gan shi da shigar nasara.
ENG; Cocky young person who wears western dress (A turance tana nufin gaye)
Gayya - Tana nufin taro ko mutane da yawa.
Misali; Samarin yankin na yin aikin gayya a kowane mako.
ENG; Communal Work (A turance tana nufin gayya)
Gayya - Tana nufin da gangan ko ana sane.
Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa.
ENG: Things done or said intentionally (A turance tana nufin gayya)
Gayyata - Tana nufin kira zuwa wani sha'ani, wato sanar da mutum cewa ana buƙatar ya zo.
Misali; Malaman sun samu saƙon gayyata ne daga hukumar ilimi ta ƙasa.
ENG; Invite (A turance tana nufin gayyata)
Gaza - Tana nufin kasawa.
Misali; Sakamakon da ya samu ya gaza kai wa yanda za a ɗuake shi a jami'a.
ENG; Fail To Do (A turance tana nufin gaza)
Gaɓar Teku - Iyaka ko fadin inda kasa, kamar najeriya take iko da shi a cikin teku.
Gaɗa - Tana nufin tafi da waƙe-waƙe da 'yanmata ke yi musamman a dandali.
Misali; 'Yanmatan sun shirya gaɗa saboda murnar bikin ƙawarsu.
ENG; Girl's game of clapping and singing (A turance tana nufin gaɗa)
Gefe - Tana nufin wani sashe.
Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya.
ENG; Side (A turance tana nufin gefe)