Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Garke - Tana nufin dabbobi da yawa, kamar akuyoyi, shanu da sauransu.
Misali; Yana da shanu garke guda.
ENG; Herd/Flock (A turance tana nufin garke)
Garma - Tana nufin ƙaton gatari mai faffaɗan kai.
Misali; Gatari ba zai yi aikin nan ba sai dai a sa garma.
ENG; Large hoe with wide blade (A turance tana nufin garma)
Garu - Tana nufin bango.
Misali; Ƙadangare yana yawo a juikin garu.
ENG; Wall (A turance tana nufin garu)
Garwashi - Tana nufin diddigar wuta.
Misali; Ta yi amfani da garwashi wajen gasa cibiyar jaririn.
ENG; Hot Embers (A turance tana nufin garwashi)
Garɗi - Tana nufin wani nau'in ɗanɗano mai daɗi a baki.
Misali; Madarar tana da garɗi sosai.
ENG; Nutty Flavour (A turance tana nufin garɗi)
Gas Exporting Countries Forum (GECF) - Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Iskar Gas
Gasa - Tana nufin gwaji ko auna tsakanin abubuwa guda biyu don fitar da wanda ya fi.
Misali; An sa gasa tsakanin 'yan aji biyu da 'yan aji uku.
ENG; Competition (A turance tana nufin gasa)
Gashi - Tana nufin tsiron da ke fitowa a saman fatar ɗan Adam ko dabba.
Misali; Mata sun fi maza yawan gashi.
ENG; Hair (A turance tana nufin gashi)
Gaskata - Tana nufin yarda.
Misali; Mun gaskata annabinmu SAW.
ENG; Believe (A turance tana nufin gaskata)
Kishiyarta; Ƙaryata
Gaskiya - Tana nufin abinda yake na haƙiƙa ma'ana yanda yake babu ƙari babu ragi.
Misali; Idan mutum na faɗin gaskiya kimarsa na ƙaruwa.
ENG; Truth (A turance tana nufin gaskiya)
Kishiyarta; Ƙarya