Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Greeting - A turance tana nufin barka.
Misali; Ina yi muku barka da yamma.
HAU; Barka (Tana nufin gaisuwa)
Grey Hair - A turance tana nufin furfura.
Misali; Furfura ta mamaye gashin mahaifina.
HAU; Furfura (Tana nufin farin gashi wanda ke fitowa mutum sakamakon tsufa ko baiwa)
Grind Coarsely - A turance tana nufin ɓarza.
Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma.
HAU; Ɓarza (Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba)
Gudanarwa - Yadda ake tafiyar da aiki ko wani al'amari bisa wani tsari da dokoki na musamman.
Guild - Kadaura, Ƙungiya, Majalisa
Guinea Corn - A turance tana nufin dawa.
Misali; Tuwon dawa na ƙara lafiya saboda tana ƙunshe da sinadarai masu inganta lafiya.
HAU: Dawa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in hatsi)
Gum - A turance tana nufin danƙo.
Misali; Hannayensa danƙo suke saboda ya sha alawa.
HAU; Danƙo (Tana nufin abu mai mannewa)
Gun - A turance tana nufin bindiga.
Misali; Sojoji sun kama wani matafiyi da bindiga a hanyar Sokoto.
HAU; Bindiga (Tana nufin na'aurar harbi musamman ga mayaƙa ko maharba ko jami'an tsaro)
Gurguzu - Tsarin siyasa ne da tattalin arziki, inda gwamnati take mallakar dukiyar kasa gabaDaya tare da jan ragamar harkokin masana'antu da kasuwanci maimakon attajirai da'yankasuwa.