Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gammo - Tana nufin tsumman da ake nannaɗawa a sa a saman kai idan za a ɗauki kaya.
Misali; Ka sa gammo a kanka saboda kayan na da nauyi.
ENG; Head Pad (A turance tana nufin gammo)
Gamsheƙa - Tana nufin ƙaton baƙin maciji.
Misali; Mun ga gamsheƙa a hanyar gonar Malam Mudi.
ENG: Black-hooded Cobra (A turance tana nufin gamsheƙa)
Ganawa - Tana nufin tattaunawar sirri ko ta musamman.
Misali; Shugaban makarantar na ganawa da malamai a ofishinsa.
ENG; Private Discussion (A turance tana nufin ganawa)
Gane - Tana nufin fahimta.
Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi?
ENG; Understand (A turance tana nufin gane)
Kishiyarta; Rashin Ganewa
Ganganci - Tana nufin yin abu ba tare da kula ba ko gaba-gaɗi.
Misali; Tuƙin gangancin da direban yake yi ne ya janyo hatsarin.
ENG; Acting in a careless way (A turance tana nufin ganganci)
Ganima - Tana nufin kayayyakin da ake samu bayan kammala yaƙi, kamar bayi, kuɗi da sauransu.
Misali; An samu ganima mai yawa a yaƙin.
ENG; Booty (A turance tana nufin ganima)
Gansakuka - Tana nufin wani koren abu da yake fitowa a guraren da danshi yake.
Misali; Bangon duk ya yi gansakuka saboda damina.
ENG;Green slime collecting on stagnant water (A turance tana nufin gansakuka)
Gantali - Tana nufin tsananin yawo.
Misali; Mijin ya saki matar ne saboda tana da gantali.
ENG; Aimless Wandering (A turance tana nufin gantali)
Ganuwa - Tana nufin ginin da ake yi don katange gari da ba shi kariya.
Misali; An ɗauki shekaru ana gina ganuwar Jihar Kano.
ENG; Town Wall (A turance tana nufin ganuwa)
Ganɗa - Tana nufin saman bakin mutum.
Misali; Ƙuraje sunm fito masa a saman ganɗa, sun hana shi cin abinci.
ENG; Roof Of The Mouth (A turance tana nufin ganɗa)