Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gyatuma - Tana nufin tsohuwar mace.
Misali; Na ga gyatumarka a bikin gidanmu.
ENG; Old Woman (A turance tana nufin gyatuma)
Kishiyarta; Gyatumi
Gyauro - Tana shukar da take fitowa a gona ko wani guri bayan an yar da ƙwallo ko iri.
Misali; Mangwaron gyauro ne, kawai fitowa ya yi a ƙofar gida.
ENG: Plants growing in farm from seeds unintentionally dropped on the ground (A turance tana nufin gyauro)
Gyauto - Tana nufin babban zani na mata.
Misali; Ta ɗaura gyauto mai matuƙar kyau da tsada.
ENG; Woman's Large Wrapper (A turance tana nufin gyauto)
Gyaɗa - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abin ci mai ɗauke da sinadaren gina jiki, ana sarrafa ta ta hanyoyi daban-daban.
Misali; Ina son dafaffiyar gyaɗa.
ENG; Groundnut (A turance tana nufin gyaɗa)