Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gidauniyar Haɗin Guiwar Bunƙasa Sabuwar Afirka - New Partnership for Africa's Development (NEPAD)
Gidauniyar Kyautata Tattalin Arziki da Zumunta - Socio-Economic Rights & Accountability Project (SERAP)
Gift from God - A turance tana nufin baiwa. Misali; Yaran aji ɗaya suna da baiwa ta musamman, don suna saurin gane karatu. HAU; Baiwa (Tana nufin wani abu na musamman da Allah yake ba wa bayinsa wanda ya bambanta su da sauran mutane)
Goats - A turance tana nufin jam'in akuya. Misali; Kaka yana kiwon awaki. HAU; Awaki (Jam'in akuya)
Gona - Gona wuri ne da ake shuka abinci da kuma kayan marmari ( kayan lambu) kamar su tumatur,kabeji,alayyahu,shinkafa,masara,dawa,gero da dai sauransu.
Graduate Internship Scheme (GIS) - Shirin Samarwa Yayayyun Dalibai Madogara
Greeting - A turance tana nufin barka. Misali; Ina yi muku barka da yamma. HAU; Barka (Tana nufin gaisuwa)
Gudanarwa - Yadda ake tafiyar da aiki ko wani al'amari bisa wani tsari da dokoki na musamman.
Guild - Kadaura, Ƙungiya, Majalisa
Gurguzu - Tsarin siyasa ne da tattalin arziki, inda gwamnati take mallakar dukiyar kasa gabaDaya tare da jan ragamar harkokin masana'antu da kasuwanci maimakon attajirai da'yankasuwa.
1 2