Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Gyara - Tana nufin daidaita abu ko mayar da abu yanda ya kamata. Misali; An gyara mana titin garinmu. ENG; Repair (A turance tana nufin gyara) Kishiyarta; Ɓatawa
Gyare - Tana nufin tsanya. Wani ƙwaro mai ƙara da daddare. Misali; Ƙarar gyare na damuna idan dare ya yi. ENG; Cricket (A turance tana nufin gyare)
Gyartai - Tana nufin mai gyaran ƙwarya. Misali; Babansa gyartai ne tun shekarun baya. ENG; Calabash Mender (A turance tana nufin gyartai)
Gyatsa - Tana nufin wata iska mai ƙara da ke fitowa daga maƙogwaro musamman idan an ƙoshi ko ana jin yunwa. Misali; Na yi gyatsa amma yunwa nake ji ba ta ƙoshi ba ce. ENG; Belching (A turance tana nufin gyatsa)
Gyatuma - Tana nufin tsohuwar mace. Misali; Na ga gyatumarka a bikin gidanmu. ENG; Old Woman (A turance tana nufin gyatuma) Kishiyarta; Gyatumi
Gyauro - Tana shukar da take fitowa a gona ko wani guri bayan an yar da ƙwallo ko iri. Misali; Mangwaron gyauro ne, kawai fitowa ya yi a ƙofar gida. ENG: Plants growing in farm from seeds unintentionally dropped on the ground (A turance tana nufin gyauro)
Gyauto - Tana nufin babban zani na mata. Misali; Ta ɗaura gyauto mai matuƙar kyau da tsada. ENG; Woman's Large Wrapper (A turance tana nufin gyauto)
Gyaɗa - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abin ci mai ɗauke da sinadaren gina jiki, ana sarrafa ta ta hanyoyi daban-daban. Misali; Ina son dafaffiyar gyaɗa. ENG; Groundnut (A turance tana nufin gyaɗa)
1 17 18 19