Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gurji - Tana nufin wani nau'i na kayan lambu mai kama da kwakunba amma ya fi ta girma.
Misali; Gurji yana da daɗi idan an kwaɗanta shi da ƙuli-ƙuli.
ENG; Cocumber-like Vegetable (A turance tana nufin gurji)
Gurnani - Tana nufin gunji da dabbobi ke yi musamman kare da zaki.
Misali; Ba zan iya shiga gidan ba, na jiyo kare yana gurnani.
ENG; Growling (A turance tana nufin gurnani)
Guɗa - Tana nufin wani salo na sarrafa ihu da mata ke yi musamman a lokutan farin ciki.
Misali; Matan sun kaure da guɗa a lokacin da aka shigo da amaryar.
ENG; Shrilling done by women to express joy (A turance tana nufin guɗa)
Gwarje - Tana nufin maɗauri da ake ratayawa a wuyan doki.
Misali; Dokinsa yana da gwarje a wuya kodayaushe.
ENG; Bell usually hung round donkey's neck (A turance tana nufin gwarje)
Gwarzo - Tana nufin mai ƙwazo.
Misali; Abdulhamid shi ne gwarzon wannan shekarar.
ENG; Person of great energy (A turance tana nufin gwarzo)
Gwauro - Tana nufin wanda a halin yanzu ba shi da aure amma ya taɓa aure.
Misali; Gwauro ne shi yanzu, ya saki matarsa a watan da ya gabata.
ENG; Unmaried person who was formally married (A turance tana nufin gwauro)
Kishiyarta; Mai Aure
Gwaza - Tana nufin makani.
Misali; Na gamu da mai siyar da gwaza da fita kasuwa.
ENG; Coco-yam (A turance tana nufin gwaza)
Gwiwa - Tana nufin sashen jiki da ke tsakanin ƙafa da cinya.
Misali; Ciwon gwiwa yake yi tunda shekarunsa suka ja.
ENG; Knee (A turance tana nufin gwiwa)
Gyale - Tana nufin mayafi ko abin rufe jiki na mata.
Misali; Kande ta yafa sabon gyale.
ENG; Woman's Shawl (A turance tana nufin gyale)
Gyambo - Tana nufin ciwon da ba ya warkewa ko kuma ya daɗe bai warke ba.
Misali; Ai gyambon da ke ƙafarsa ya daɗe sosai.
ENG; Ulcerated Wound (A turance tana nufin gyambo)