Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gunduma - Tana nufin ɗibgawa ko yi wa mutum gagarumin laifi.
Misali; An gunduma wa 'yan kasuwar sata.
ENG; Do much of evil act (A turance tana nufin gunduma)
Gundura - Tana nufin jin abu ya fita daga rai.
Misali; Kallon wasan ƙwallon ƙafa ya gundure ni.
ENG; Lose Interest (A turance tana nufin gundura)
Gunki - Tana nufin sassaƙaƙƙen abu musamman wanda ake bautawa, zai iya kasancewa mai siffar mutum ko dabba da sauransu.
Misali; Indiyawa na da gunki a gidajensu, don sun yarda shi ne abin bautarsu.
ENG; Idol (A turance tana nufin gunki)
Guntu - Tana nufin mara tsayi.
Misali; Da wani guntun itace na ƙarasa girkin.
ENG; Short (A turance tana nufin guntu)
Kishiyarta; Dogo/ Mai tsayi
Guntule - Tana nufin yanke wani sashi.
Misali; A musulunci hukuncin sata shi ne guntule hannu.
ENG; Cut Short (A turance tana nufin guntule)
Gurasa - Tana nufin nau'in abinci da ake yi da fulawa kuma gasa ta ake yi a tanderu.
Misali; Na yi banɗashen gurasa a matsayin abincin rana.
ENG; Baked-wheat cake (A turance tana nufin gurasa)
Gurfana - Tana nufin durƙusawa a kan gwuiwa biyu.
Misali; Masu laifin sun gurfana a gaban alƙali.
ENG; Kneel with front elbows on ground (A turance tana nufin gurfana)
Gurgu - Tana nufin wanda ba shi da ƙafa.
Misali; Ya zama gurgu ne sanadiyyar hatsarin motar da suka yi.
ENG; Cripple (A turance tana nufin gurgu)
Kishiyarta; Mai ƙafa
Gurguzu - Tsarin siyasa ne da tattalin arziki, inda gwamnati take mallakar dukiyar kasa gabaDaya tare da jan ragamar harkokin masana'antu da kasuwanci maimakon attajirai da'yankasuwa.
Guringuntsi - Tana nufin ƙashi mai laushi da ke jikin ɗan Adam da dabba.
Misali; Guringuntsi na da daɗi musamman a miyar taushe.
ENG; Cartilage (A turance tana nufin guringuntsi)