Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Guava - A turance tana nufin goba.
Misali; Goba tana da sinadarai masu inganta lafiya a cikinta.
HAU; Goba (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari tana da ƙananan ƙwallaye a cikinta)
Guba - Tana nufin duk wani abin da zai iya kisa.
Misali; Na sa wa ɓeraye guba jiya da yamma.
ENG; Poison (A turance tana nufin guba)
Guda - Tana nufin ɗaya.
Misali; Gida guda za mu zauna da ƙani na.
ENG; One (A turance tana nufin guda)
Gudanar - Tana nufin aiwatarwa.
Misali; An gudanar da taron a gidan adana ababen tarihi.
ENG; Administer (A turance tana nufin gudanar)
Gudanarwa - Yadda ake tafiyar da aiki ko wani al'amari bisa wani tsari da dokoki na musamman.
Gudawa - Tana nufin yin bayan gida (kashi) akai-akai kuma mai ruwa-ruwa, a wasu lokutan ma har da ciwon ciki.
Misali; Tun jiya yake gudawa amma ya sha magani yanzu.
ENG; Diarrhoea (A turance tana nufin gudawa)
Gudu - Tana nufin tafiya da ƙololuwar sauri.
Misali; Idan ka yi gudu zuciyarka na harbawa da sauri.
ENG; Run (A turance tana nufin gudu)
Guduma - Tana nufin abin da ake amfani da shi wajen buga katako ko ƙusa da sauransu.
Misali; Ya buge hannu da guduma a lokacin da yake gyaran kujerar.
ENG; Hammer (A turance tana nufin guduma)
Gudunmawa - Tana nufin tallafi ko agaji.
Misali; Gwamnati ta kawo gudunmawa ga waɗanda ibtila'in gobara ya afkawa.
ENG; Help (A turance tana nufin gudunmawa)
Guguwa - Tana nufin iska mai ƙarfi.
Misali; Bishiyar ta faɗo ne yayin da ake guguwa.
ENG; Whirlwind (A turance tana nufin guguwa)