Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Grass - A turance tana nufin ciyawa.
Misali;Ciyawa ta fito a gonar sosai, dole sai an cire ta kafin yi shuka.
HAU; Ciyawa (Tana nufin tsiron da yake fitowa ba tare an shuka shi ba, tana da siraran ganye koraye)
Grass - A turance tana nufin ciyawa.
Misali; Na samo hakin da zan yi amfani da shi don yin maganin.
HAU; Haki (Tana nufin ciyawa)
Grave - A turance tana nufin kabari.
Misali; Ya daɗe yana sana'ar haƙar kabari.
HAU; Kabari (Tana nufin ramin da ake binne mamaci)
Greed - A turance tana nufin haɗama.
Misali; Saboda haɗama ya kwashe abincin mutum uku shi kaɗai.
HAU; Haɗama (Tana nufi wawashe abu da yawa musamman idan ana haɗawa da rabon wasu)
Green slime collecting on stagnant water - A turance tana nufin gansakuka.
Misali; Bangon duk ya yi gansakuka saboda damina.
HAU; Gansakuka(Tana nufin wani koren abu da yake fitowa a guraren da danshi yake)
Greeting - A turance tana nufin barka.
Misali; Ina yi muku barka da yamma.
HAU; Barka (Tana nufin gaisuwa)
Grey Hair - A turance tana nufin furfura.
Misali; Furfura ta mamaye gashin mahaifina.
HAU; Furfura (Tana nufin farin gashi wanda ke fitowa mutum sakamakon tsufa ko baiwa)
Grind Coarsely - A turance tana nufin ɓarza.
Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma.
HAU; Ɓarza (Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba)
Groundnut - A turance tana nufin gyaɗa.
Misali; Ina son dafaffiyar gyaɗa.
HAU; Gyaɗa (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abin ci mai ɗauke da sinadaren gina jiki, ana sarrafa ta ta hanyoyi daban-daban)
Growling - A turance tana nufin gurnani.
Misali; Ba zan iya shiga gidan ba, na jiyo kare yana gurnani.
HAU; Gurnani (Tana nufin gunji da dabbobi ke yi musamman kare da zaki)