Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Good News - A turance tana nufin bishara.
Misali; Malamin ya yi wa ɗalibai bishara da cinye jarabawarsu.
HAU; Bishara (Tana nufi labari mai daɗi)
Goro - Tana nufin ɗan itaciya da ake ci mai ƙunshe da muhimman abubuwa masu inganci.
Misali; An raba goro a gurin ɗaurin auren.
ENG; Kolanut (A turance tana nufin goro)
Goshi - Tana nufin gaɓar da ke saman gira.
Misali; Ya fasa goshi garin wasan banza.
ENG; Forehead (A turance tana nufin goshi)
Gourd Water Bottle - A turance tana nufin jallo.
Misali; Jauro ya shanye ruwan cikin jallo na, sai na ɗebo wani.
HAU; Jallo (Tana nufin mazubin ruwa na duma)
Government Body/Authority - A turance tana nufin hukuma.
Misali; Hukuma ce ke da ikon hukunta wanda ya karya dokar ƙasa.
HAU; Hukuma (Tana nufin gwamnati ko waɗanda ke da ƙarfin iko, da shugabancin al'umma a ƙasa da jiha da ƙananan hukumomi)
Graduate Internship Scheme (GIS) - Shirin Samarwa Yayayyun Dalibai Madogara
Grain - A turance tana nufin hatsi.
Misali; Akwai rumbun hatsi a gidan maigari.
HAU; Hatsi (Tana nufin tsabar abinci kamar gero, masara, dawa da sauransu)
Grandchild - A turance tana nufin jika.
Misali; Maƙoci na ya yi jika, jiya 'yarsa ta haihu.
HAU; Jika (Tana nufin yaro ko yarinyar da ɗa ko 'ya suka haifa)
Grapes - A turance tana nufin inibi.
Misali; Inibi yana da tsada sosai don kawo shi ake daga ƙasashen ƙetare.
HAU; Inibi (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari)
Grasp With Hand - A turance tana nufin danƙa.
Misali; Ya sha danƙa a gurin 'yan sanda kuma jikinsa zai gaya masa.
HAU; Danƙa(Tana nufin kamo mutum da hannu)