Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Gobe - Tana nufin bayan kwana guda ma'ana ranar da za biyo bayan wacce ake ciki.
Misali; Gobe babu karatu saboda hutun ƙarshen mako.
ENG; Tomorrow (A turance tana nufin gobe)
Kishiyarta; Yau
God - A turance tana nufin jalla.
Misali; Allah jalla wa azza ne ya nufa za a yi ruwa mai yawa yau.
HAU; Jalla (Tana nufin Allah maɗaukakin sarki)
Godiya - Tana nufin yabawa.
Misali; Mun yi wa babanmu godiya ranar da ya siyo mana kayan salla.
ENG: Thanks (A turance tana nufin godiya)
Kishiyarta; Rashin Godiya
Gogagge - Tana nufin ƙwarewa a wani abu ko wani fanni.
Misali; Ai malamin gogagge ne a fannin kimiyya da fasaha.
ENG; Skilled (A turance tana nufin gogagge)
Going back and forth - A turance tana nufin jigila.
Misali; Kamfanonin jiragen sama na ta jigilar alhazai daga ƙasashe daban-daban.
HAU; Jigila (Tana nufin kai wa da komowa (kai-komo))
Going to and fro - A turance tana nufin jewa.
Misali; Na gan shi yana ta jewa saboda tashin hankali.
HAU; Jewa (Tana nufin je-ka-ka-dawo)
Goma - Tana nufin lambar da ke bin bayan tara.
Misali; Littattafai goma ne a cikin jakar.
ENG; Ten (A turance tana nufin goma)
Gomiya - Tana nufin goma sau wani adadi.
Misali; Gomiya biyar tana nufin hamsin kenan.
ENG; Multiple Of Ten (A turance tana nufin gomiya)
Gona - Gona wuri ne da ake shuka abinci da kuma kayan marmari ( kayan lambu) kamar su tumatur,kabeji,alayyahu,shinkafa,masara,dawa,gero da dai sauransu.
Gona - Tana nufin fili ko sararin da ake shuka a yi noma.
Misali; Yana da gona amma ya gaje ta ne a gurin mahaifinsa.
ENG; Farm (A turance tana nufin gona)