Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ginsa - Tana nufin isa ko fita daga rai.
Misali; Cin abinci nau'i ɗaya kullum na da ginsa.
ENG; Have as much as one can stand (A turance tana nufin ginsa)
Ginshiƙi - Tana nufin jigo ko tushe.
Misali; Imani shi ne ginshiƙin addini.
ENG; Pillar supporting a roof (A turance tana nufin ginshiƙi)
Gira - Tana nufin gurbin da ke tsakanin ido da goshi, yana ɗauke da gashi amma ba mai yawa ba.
Misali; Haramun ne aske gashin gira a musulunci.
ENG; Eyebrow (A turance tana nufin gira)
Girbi - Tana nufin kwashe amfanin gona bayan ya gama nuna.
Misali; Manoman na cikin farin ciki sakamakon lokacin girbi ya yi.
ENG; Reap (A turance tana nufin girbi)
Girgije - Tana nufin gajimaren da yake ɗauke da ruwa.
Misali; Girgije ya lulluɓe sararin samaniya.
ENG; Rain-Cloud (A turance tana nufin girgije)
Girgiɗe - Tana nufin cire abu da ƙarfi.
Misali; An girgiɗe mata haƙorin don ya ishe ta da ciwo.
ENG; Uproot By Shaking (A turance tana nufin girgiɗe)
Girka - Tana nufin ɗora tukunya a kan wuta.
Misali; Ta girka tukunya, ba za mu tafi ba sai ta sauke.
ENG; Putting a pot on the fire (A turance tana nufin girka)
Girl friend/ Unmarried girl of marriageable age - A turance tana nufin budurwa.
Misali; Fiddausi ta zama budurwa, baɗi za a yi mata aure.
HAU; Budurwa (Tana nufin yarinyar da ta isa aure)
Gishiri - Tana nufin sinadarin da ke ba wa abinci ɗanɗano.
Misali; Kirarinsa shi ne: Gishiri in ba kai ba miya.
ENG: Salt (A turance tana nufin gishiri)
Giving much effort for little gain - A turance tana nufin haƙilo.
Misali; Ɗaliban na ta haƙilo don ganin ba su faɗi jarrabawa ba.
HAU; Haƙilo (Tana nufin yin abu da gaske ka'in da na'in, tare da kai komo)