Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙware - Tana nufin shaƙewa ko toshewar maƙogwaro ta yadda numfashi ko haɗiyar abinci zai yi wuya.
Misali: Yaron ya ƙware da abinci.
ENG: Choke (A turance tana nufin ƙware)
Ƙwaƙule - Tana nufin fito da wani abu daga cikin wani abu ta hanyar hako, ko ƙwakkwafe shi daga ciki.
Misali: Dodannin na ƙwaƙule idanun dabbobin da suka kama.
ENG: Scrape Out from Inside (A turance tana nufin ƙwaƙule)
Ƙwaƙwa - Tana nufin yawan yin tambayoyi, son sani, ko binciken abubuwa domin samun ƙarin bayani da fahimta.
Misali: Yaron yana da ƙwaƙwa sosai, domin kullum yana tambayar abubuwan da yake ji da gani.
ENG: Being Inquisitive (A turance tana nufin ƙwaƙwa)
Ƙwaƙwalwa - Tana nufin sashen jiki da ke cikin kwanya wanda ke sarrafa tunani, fahimta, motsi, da sauran ayyukan jiki.
Misali: Karatu na taimakawa wajen haɓaka ƙwaƙwalwa.
ENG: Brain (A turance tana nufin ƙwaƙwalwa)
Ƙwaƙƙwafi - Bin diddigi domin gano wani ɓoyayyen al'amari.