Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ƙurungu - Ƙurungu wani nau’in kifi ne mai gemu da tabo a jikinsa, wanda ake samu a kogi da tafki. Misali: Masunci ya kama ƙurungu a kogi yau da safe. ENG: Spotted Catfish (A turance tana nufin ƙurungu)
Ƙusa - Tana nufin wani nau'in ƙarfe mai tsini daga ƙarshensa wanda ake amfan da shi wajen haɗe katako ko a buga a bango don rataye abu. Misali: Kafintan ya buga ƙusa a jikin bencin da ya karye. ENG: Nail (A turance tana nufin ƙusa)
Ƙusumbi - Tana nufin tudun nama da yake bayan mutum ko wasu dabbobi kamar raƙumi da sauransu. Misali: Raƙumi yana da ƙusumbi a bayansa wanda yake adana kitse. ENG: Hump (A turance tana nufin ƙusumbi)
Ƙuƙuta - Tana nufin yin iya bakin ƙoƙari ko dagewa sosai domin cimma wani buri ko kammala wani aiki. Misali: Ya ƙuƙuta matuƙa wajen neman ilimi har ya samu nasara. ENG: Try Hard (A turance tana nufin ƙuƙuta)
Ƙwace - Tana nufin karɓe abu daga hannun wani da ƙarfi ko ba tare da izininsa ba. Misali: Ɓarayin sun ƙwace wayarsa a kan hanya da dare. ENG: Take by Force (A turance tana nufin ƙwace)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwafa - Tana nufin yin wani sauti daga makogwaro ko harshe domin nuna fushi, ɓacin rai, ko rashin jin daɗi. Misali: Da ya ji abin da aka faɗa masa, sai ya yi ƙwafa ya juya ba tare da ya ce komai ba. ENG: Clicking sound made in the throat to indicate anger (A turance tana nufin ƙwafa)
Ƙwai - Tana nufin abin da tsuntsaye da wasu dabbobi ke yi wanda ke ɗauke da ɗa, kuma ana amfani da shi a matsayin abinci. Dabbobin da tsuntsayen kan yi ƙwai a madadin haihuwa. Misali: Ta dafa ƙwai biyu domin karin kumallo. ENG: Egg (A turance tana nufin ƙwai)
Ƙwainanuwa - Tana nufin yarinya mai hankali, basira, da fahimta fiye da yadda ake tsammani a shekarunta. Misali: Aisha ƙwainanuwa ce, domin tana yin magana da hikima da tunani duk da ƙanƙantar shekarunta. ENG: Wise Young Girl (A turance tana nufin ƙwainanuwa)
Ƙwala - Tana nufin yin kira da ƙarfi ko bugawa mutum wani abu. Misali: Sun dawo bayan Ibrahim ya ƙwala musu kira. ENG: Resound (A turance tana nufin ƙwala)
1 15 16 17 18 19