Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ɓuntu - Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki.
Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai.
ENG; Husks of Rice (A turance tana nufin ɓuntu)
Ɓuruntu - Tana nufin ɓare-ɓare da hayaniya.
Misali; Ɓera yana ta ɓuruntu a ɗakin Kaka.
ENG; Looting in a noisy manner (A turance tana nufin ɓuruntu)