Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Road Transport Employers’ Association of Nigeria (RTEAN) - Ƙungiyar Direbobi Ta Najeriya
Road/ Path - A turance tana nufin hanya. Misali; Gwamnati ta gina hanya a tsakanin ƙauyukan guda biyu. HAU; Hanya (Tana nufin guri ko inda ake wucewa)
Roaming about leading a loose, carefree life - A turance tana nufin dandi. Misali; Ta dawo daga yawon dandi ɗauke da cuta mai tsanani. HAU: Dandi (Tana nufin yawo da rayuwa ta rashin mafaɗi)
Rolling on the ground - A turance yana nufin birgima. Misali; Yaron yana ta birgima don an hana shi fita wasa. HAU; Birgima (Tana nufin a yi ta juyi a ƙasa)
Roof Of The Mouth - A turance tana  nufin ganɗa. Misali; Ƙuraje sunm fito masa a saman ganɗa, sun hana shi cin abinci. HAU; Ganɗa (Tana nufin saman bakin mutum)
Rope - A turance tana nufin igiya. Misali; Na gama wankin zan shanya a kan igiya yanzu. HAU; Igiya (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin shanyar kaya ko ɗaure abubuwa)
Rubber Research Institute of Nigeria (RRIN) - Cibiyar Binciken Noman Roba Ta Najeriya
Rule/Law - A turance tana nufin doka. Misali; Duk wanda ya karya doka sai an masa hukunci. HAU: Doka (Tana nufin ƙa'idoji ko tsare-tsare)
Rumour - A turance tana nufin jita-jita. Misali; Ya shahara wajen yaɗa jita-jita, sai dai mu yi masa fatan shiriya. HAU; Jita-jita (Tana nufin zancen da ba shi da tabbas)
Run - A turance tana nufin gudu. Misali; Idan ka yi gudu zuciyarka na harbawa da sauri. HAU;Gudu (Tana nufin tafiya da ƙololuwar sauri)
1 3 4 5 6