Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Removal of things to another location - A turance tana nufin jido.
Misali; Mun jido kayan daga tsohon gida zuwa sabo.
HAU; Jido (Tana nufin ɗebo kaya daga wani guri zuwa wani gurin)
Repair - A turance tana nufin gyara.
Misali; An gyara mana titin garinmu.
HAU; Gyara (Tana nufin daidaita abu ko mayar da abu yanda ya kamata)
Kishiyarta; Ɓatawa
Repeat - A turance tana nufin kuma.
Misali; Yanzu zazzaɓi ba ya jin magani ko kin sha sai kin kuma sha.
HAU; Kuma (Tana nufin sake yi ko maimaitawa)
Repeatedly - A turance tana nufin bini-bini.
Misali; Abokina bini-bini ya zo gidanmu, hakan ya sa mun shaƙu.
HAU; Bini-bini (Tana nufin akai-akai)
Reporters Without Borders - Tawagar Manema Labarai/'Ƴanjarida Marasa Shamaki
Republic - A turance tana nufin jamhuriya.
Misali; Jamhuriyar Niger ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za a yi amfani da shi a ƙasar.
HAU; Jamhuriya (Tana nufin ƙasar da ke da tsarin mulki na musamman)
Rest/Holiday - A turance tana nufin hutu.
Misali; Yara ba sa zuwa makaranta saboda an ba su hutu.
HAU; Hutu (Tana nufin zama guri ɗaya ba tare da aikin komai ba ko rashin zuwa gurin aiki ko makaranta ko gyurin sana'a na wani lokaci don a tsahirta kafin a ɗora)
Reticence - A turance tana nufin kawaici.
Misali; Laure tana da kawaici shi yasa suke mata abinda suka ga dama.
HAU; Kawaici (Tana nufin ɗauke kai ko yin shiru a kan abinda ya kama mutum ya yi magana amma sai ya yi shiru)
Revenue Mobilization, Allocation & Fiscal Commission (RMAFC) - HukumarTattarowa da Kasafta Haraji Ta Ƙasa
Rhinoceros - A turance tana nufin karkanda.
Misali; Ba a ganin karkanda sai a ƙungurmin daji.
HAU; Karkanda (Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin daji mai matuƙar ƙarfi)