Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Examination - A turance tana nufin jarrabawa.
Misali; Suna gama jarrabawa za a ba su hutu.
HAU; Jarrabawa (Tana nufin gwaji)
Except - A turance tana nufin face.
Misali; Babu wanda zai makara face ya kasance mai saɓa alƙawari.
HAU; Face (Tana nufin sai dai)
Excessive Desire - A turance tana nufin jaraba.
Misali; Shan giya ya zama jaraba gare shi, sai ya sha yake jin daɗi.
HAU; Jaraba (Tana nufin jin so mai tsanani)
Excessive Fat - A turance tana nufin ɓulɓul.
Misali; Jamila ta yi ɓulɓul tunda ta dawo daga Ikko.
HAU; Ɓulɓul (Tana nufin ƙiba sosai)
Executioner - A turance tana nufin hauni.
Misali; Ɓarayin sun gamu da hauni a kotu.
HAU; Hauni (Tana nufin mai yanke hukuncin kisa)
Explain Thoroughly - A turance tana nufin fayyace.
Misali; Malamin ya fayyace mana darasin dalla-dalla.
HAU; Fayyace (Tana nufin yin cikakken bayani)
Explanation - A turance yana nufin bayani.
Misali; Malami yana yi wa ɗalibai bayani akan darasin larabci.
HAU; Bayani (Tana nufin yin magana don fahimtarwa)
Extreme Degree - A turance tana nufin innanaha.
Misali; Ai munafiki ne na innanaha.
HAU; Innanaha (Tana nufin ƙololuwa)
Extreme End - A turance tana nufin gaya.
Misali; Yaran sun yi ƙoƙari matuƙa gaya.
HAU; Gaya (Tana nufin ƙololuwa ko ƙarshe)
Eye - A turance tana nufin ido.
Misali; Ido na ɗaya daga cikin sashen jiki mafi muhimmanci.
HAU; Ido (Tana nufin gaɓar da ake gani da ita)