Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Prophet - A turance yana nufin wanda Allah ya aiko.
Misali; Shugaban annabawa shi ne annabi Muhammad (S.A.W)
HAU; Annabi (Wanda Allah ya aiko da saƙon addini)
Prostitute - A turance tana nufin karuwa.
Misali; Ku karanta ƙissar karuwa da karen da ta ba wa ruwa, akwai darasi.
HAU; Karuwa (Tana nufin mace mai zaman kanta)
Protection - A turance tana nufin kandagarki.
Misali; Ya yi wa kansa kandagarki don ya san zai daku.
HAU; Kandagarki (Tana nufin kariya)
Proverb - A turance tana nufin karin magana.
Misali; Darasin da malamin Hausa ya koyar yau shi ne karin magana.
HAU; Karin Magana (Tana nufin zance na hikima mai ƙunshe da nuni ko habaici wanda ake yi don azanci ko huce haushi)
Psychology Association of Nigeria (PAN) - Ƙungiyar Masana Mutuntaka Ta Najeriya
Puberty - A turance tana nufin balaga.
Misali; Idan yara sun balaga halayensu kan canja kuma iyaye sai sun dage matuƙa wajen tarbiyya a wannan lokacin.
HAU; Balaga (Tana nufin matakin girma da mace ko namiji ke kai wa, wanda yake zuwa da canje-canje a halitta da ɗabi'u)
Public Complaints Commission (PCC) - Hukumar Karɓar Ƙorafin Jama'a
Public Service Institute of Nigeria (PSIN) - Cibiyar Ƙwarewa Ta Jami'an Gwamnati
Pull out suddenly with force - A turance tana nufin fincika.
Misali; Ta tsinka jakar da ta fincika.
HAU; Fincika (Tana nufin jan abu da ƙarfi)
Pull/Drag - A turance tana nufin ja.
Misali; Ya ja igiyar da ƙarfi shi yasa ta tsinke.
HAU; Ja (Tana nufin janyowa)