Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Patience - A turance tana nufin haƙuri.
Misali; Ya samu mace mai haƙuri shi yasa zamansu ya yi tsayi.
HAU; Haƙuri (Tana nufin dangana da rashin ɗaukar mataki idan an maka laifi)
Kishiyarta; Rashin haƙuri
Paw - A turance tana nufin dagi.
Misali; Na ga shatin dagi a ƙofar gida, amma ya fi kama da na kare.
HAU; Dagi (Tana nufin tafin ƙafar dabbobi masu ƙafa huɗu kamar kare da mage da sauransu)
Pay - A turance tana nufin biya.
Misali; An biya ma'aikata albashin su na wannan watan.
HAU; Biya (Tana nufin bayar da kuɗi sakamakon wani aiki, ko bayar da wani abu a dalilin yin wani aiki)
Peace Corps of Nigeria (PCN) - Rundunar Zaman Lafiya Ta Najeriya
Pediatric Association of Nigeria (PAN) - Kungiyar Likitocin Yara Ta Najeriya
Penalty to atone for breaking certain islamic law - A turance tana nufin kaffara.
Misali; Azumi uku ake yi a kaffarar rantsuwa.
HAU; Kaffara (Tana nufin abin da mutum zai yi don karya rantsuwa ko sakamakon kisa da sauransu. Akan yi kaffara da azumi ko ciyarwa da sauransu)
Pencil - A turance tana nufin fensir.
Misali; 'Yan aji ɗaya da fensir suke rubutu.
HAU; Fensir (Tana nufin abin rubutu)
Pension - A turance tana nufin fansho.
Misali; Ma'aikata da dama da fansho suke siyan gida.
HAU; Fansho (Tana nufin kuɗin da ake ba wa mutum bayan ya kammala shekarun aikinsa)
Pepper - A turance yana nufin barkono.
Misali; Inna ta siyo barkono za ta daka yajin daddawa.
HAU; Barkono (Yana nufin tsiro daga cikin kayan lambu, yana kama da tattasai amma shi dogo ne)
Pepper Soup - A turance tana nufin farfesu.
Misali; Tunda ya fara zazzaɓi yake sha'awar farfesu.
HAU; Farfesu (Tana nufin dafa abu da romo-romo, kamar kaza ko kifi da sauransu)