Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Origin - A turance tana nufin origin.
Misali; Annabi Muhammad yana da kyakkyawan asali.
HAU; Asali (Tana nufin tushe ko mafari)
Outdoor Advertising Association Of Nigeria (OAAN) - Ƙungiyar Kamfanonin Allunan Talla Ta Najeriya
Outsider - A turance tana nufin bare.
Misali; Iliya bare ne, ba mu da dangantaka da shi.
HAU; Bare (Tana nufin wanda ba a da dangantaka ta jini da shi)
Over there - A turance tana nufin can.
Misali; Na ajiye butar a can.
HAU; Can (Tana nufin nesa da inda ake)
Overturn/ Upside down - A turance tana nufin birkice.
Misali; Ya birkice ɗakin yana neman maɓallin rigarsa.
HAU; Birkice (Tana nufin a juya abu daga sama zuwa ƙasa)