Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

One after the other - A turance tana nufin bi da bi. Misali; Likitan yana duba marasa lafiyan bi da bi. HAU; Bi da bi (Tana nufin ɗaya bayan ɗaya)
One Thousand - A turance tana nufin dubu. Misali; Ya ba ni Naira dubu da ya zo duba ni a asibiti. HAU: Dubu (Tana nufin lambar da ke bin bayan ɗari tara da casa'in da tara)
Open space in front of compound - A turance tana nufin farfajiya. Misali; A farfajiyar gidan za a yi taron bikin. HAU; Farfajiya (Tana nufin filin tsakar gida)
Open Space/Arena - A turance tana nufin fage. Misali; An ba wa 'yan dambe fage don su fafata. HAU; Fage (Tana nufin fili ko dandali)
Opportunity - A turance tana nufin faraga. Misali; Mun samu faraga mun yi abubuwan alkhairi da yawa. HAU; Faraga (Tana nufin samun dama)
Organization - Hukuma, Ƙungiya
Organization Of African Trade Union Unity (OATUU) - Gamayyar Ƙungiyar 'Ƴankasuwa Ta Afirka
Organization of Islamic Cooperation (OIC) - Kadaurar Haɗa-Kan Musulmi
Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC) - Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin Fetur
Organization Of Trade Unions of West Africa (OTUWA) - Ƙungiyar 'Ƴankasuwa Ta Yammacin Afirka
1 2 3