Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
International Institute of Islamic Thought (IIIT) - Cibiyar Yaɗa Koyarwar Musulunci Ta Duniya
International Islamic Liquidity Management Corporation (IILM) - Hukumar Gudanarwar Dukiyar Musulunci Ta Duniya
International Islamic Relief Organization (IIRO) - Ƙungiyar Agaji Ta Musulman Duniya
International Labour Organization (ILO) - Ƙungiyar Ƙwadago Ta Duniya
International Livestock Research Institute (ILRI) - Cibiyar Binciken Bisashe Ta Duniya
International Maritime Organization (IMO) - Hukumar Sufurin Teku Ta Duniya
Internationl Air Transport Association (IATA) - Ƙungiyar Jigilar Jirgin Sama Ta Duniya
Intrusiveness - A turance tana nufin katsalandan.
Misali; Makwabcinsa yana yawan yi masa katsaladan a al'amuran shi.
HAU; Katsalandan (Tana nufin shiga abin da bai shafi mutum ba ko shisshigi)
Investigation - A turance yana nufin bincike.
Misali; 'Yan sanda na bincike don gano masu aikata laifi.
HAU; Bincike (Tana nufin ƙoƙarin gano wani abu)
Invite - A turance tana nufin gayyata.
Misali; Malaman sun samu saƙon gayyata ne daga hukumar ilimi ta ƙasa.
HAU; Gayyata (Tana nufin kira zuwa wani sha'ani, wato sanar da mutum cewa ana buƙatar ya zo)