Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Independent Petroleum Marketers Association of Nigeria (IPMAN) - Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Ta Najeriya
Indigineous Languages Writers Association of Nigeria (ILWAN) - Ƙungiyar Marubuta Ta Harsunan Najeriya
Indirect Reference - A turance tana nufin habaici.  Misali; Tun safe take yi wa kishiyarta habaici. HAU; Habaici (Tana nufin magana a fakaice ba tare da ambaton suna ba, amma shi wanda ake da shi ya sani)
Industrial Training Fund (ITF) - Asusun Horon Ɗalibai na Masana'antu
Infant - A turance tana nufin jariri. Misali; An tsinci jariri a unguwarmu. HAU; Jariri (Tana nufin wanda ba a daɗe da haifa ba)
Infant - A turance tana nufin jinjiri. Misali; Jinjiri aka haifa masa shekaran jiya. HAU; Jinjiri (Tana nufin jariri) Kishiyarta; Jinjinniya
Infants - A turance tana nufin jarirai. Misali; Kayan da gwamnati ta kawo na tallafin jarirai ne. HAU; Jarirai (Tana nufin jam'in jariri)
Information Technology Association OF Nigeria (ITAN) - Ƙungiyar Masana Fasahar Bayanai Ta Najeriya
Infrastructure Concession Regulatory Commission (ICRC) - Hukumar Kyautata Samuwar Ababen More Rayuwa
Ingarma - Tana nufin babban doki ko gabjejen mutum. Misali; Dokin yarima ingarma ne. ENG; Large Stallion (A turance tana nufin ingarma)
1 2 3 4 5 6 11