Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Imitate - A turance tana nufin koyi. Misali; Koyi da annabawa kyakkyawar ɗabi'a ce. HAU; Koyi (Tana nufin kwaikwaya ko yin abinda wani ya yi)
Imma - Tana nufin ko. Misali; Ka zaɓi ɗaya, imma makarantar kwana ko ta je-ka-ka-dawo. ENG; Either/Or (A turance tana nufin imma)
Impress - A turance tana nufin burge. Misali; Samarin na ƙoƙarin yin komai don burge 'yan matan su. HAU; Burge (Tana nufin ƙoƙarin janyo ra'ayi ko yardar wani)
In’ina - Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa. Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina. ENG; Stuttering/ Stammering (A turance tana nufin in'ina)
Inda - Tana nufin gurin da abu yake. Misali; Mukullin yana inda nake ajiye kayana. ENG; Where (A turance tana nufin inda)
Inda-inda - Tana nufin rashin ƙwaƙƙwaran ra'ayi ko kokwanto. Misali; Tun ɗazu yake ta inda-inda saboda ba shi hujja a kan abinda ake tuhumarsa a kai. ENG; Behaving or talking indecisively (A turance tana nufin inda-inda)
Indararo - Tana nufin hanyar da ruwa yake zubowa ta saman rufin kwano. Misali; Mun cika gidan nan da ruwan da muka tara a indararo. ENG; Metal Roof Drain (A turance tana nufin indararo)
Indecent talk - A turance tana nufin batsa. Misali; Wasu daga cikin masu amfani da manhajar TikTok na yawan yin batsa a bidiyoyinsu. HAU; Batsa (Tana nufin zantuttuka na rashin  ɗa'a)
Independent Corrupt Practices Commission (ICPC) - Hukumar Hana Cin Hanci / Hukumar Yaki da Cin Hanci
Independent National Electoral Commission (INEC) - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta Ta Ƙasa
1 2 3 4 5 11