Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Igiya - Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin shanyar kaya ko ɗaure abubuwa.
Misali; Na gama wankin zan shanya a kan igiya yanzu.
ENG; Rope (A turance tana nufin igiya)
Ignore - A turance tana nufin biris.
Misali; Duk da yana cikin mawuyacin hali amma matarsa ta yi biris da shi saboda rashin kirkinsa.
HAU; Biris (Tana nufin nuna halin ko-in-kula da abu ko yin watsi da shi)
Ihu - Tana nufin ƙara ko fitar da sauti da ƙarfi.
Misali; Matasan na ihu ne don sun ci ƙwalo.
ENG: Yelling (A turance tana nufin ihu)
Ijaba - Tana nufin cikar buri.
Misali; Allah ya yi mana ijaba, yau ruwa ya sauka.
ENG; Fulfilment Of Wish (A turance tana nufin ijaba)
Iko - Tana nufin ƙarfi ko isa.
Misali; Shugabanni su ke da iko a kan mabiyansu.
ENG; Power/Authority (A turance tana nufin iko)
Ilahiri - Tana nufin duka ko gaba ɗaya ko bai ɗaya.
Misali; Ya shafe ilahirin jikinsa da maganin.
ENG; Whole (A turance tana nufin ilahiri)
Ilimi - Tana nufin sani.
Misali; Allah ya yi masa baiwar ilimi ƙwarai da gaske.
ENG; Knowledge (A turance tana nufin ilimi)
Illiterate Person - A turance tana nufin jahili.
Misali; Rashin zuwa makaranta ne ke mai da mutum jahili.
HAU; Jahili (Tana nufin wanda ba shi da ilimi)
Illness - A turance tana nufin cuta.
Misali; Wata sabuwar cuta ta ɓullo mai suna korona.
HAU; Cuta(Tana nufin rashin lafiya)
Imani - Tana nufin yarda, amincewa ko ba da amanna ɗari bisa ɗari.
Misali; Yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin rukunan imani.
ENG; Faith (A turance tana nufin imani)