Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Iyaye - Tana nufin mahaifi da mahaifiya.
Misali; Wajibi ne biyayya ga iyaye idan mutum yana son gamawa lafiya.
ENG; Parents (A turance tana nufin iyaye)
Izga - Tana nufin jela musamman ta doki da ake amfani da ita wajen korar ƙuda.
Misali; Da izga yake amfani don kore ƙuda daga kan kayan sana'arsa.
ENG; Tail used as fly-switch (A turance tana nufin izga)
Izgili - Tana nufin wulaƙanci ko ƙasƙantarwa musamman ga abu mai daraja.
Misali; Bayan ya yi wa iyayensa izgili rayuwarsa rugujewa ta yi.
ENG; Being Presumptuous (A turance tana nufin izgili)
Izifi - Tana nufin ɗaya daga cikin kaso sittin na Ƙur'ani.
Misali; Abdallah ya haddace izifi biyu a watan da ya gabata.
ENG; One of the sixty sections into which the Qur'an is divided (A turance tana nufin izifi)
Izini - Tana nufin dama ko yarda ko amincewa.
Misali; An ba shi izini ya fito neman auren Binta.
ENG; Permission (A turance tana nufin izini)
Izza - Tana nufin jin isa da faɗin rai.
Misali; Sarautar da aka naɗa shi ta sa shi jin izza.
ENG; Haughtiness (A turance tana nufin izza)